Kakakin Ma'ikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta fada jiya jumma’a cewa tana fatan wadannan matakai zasu kawo karshen matsalar da kasashen biyu suka shiga, lamari da yashafi wata jami’ar difilomasiyyar kasarzindia wacce hukumomin Amurka suke zargi ta kasa biyan wata ‘yar gidanta kayyadadden karamin albashi da za’a biya ma’aikaci a Amurka.
Kakakin ta Amurka bata bayyana jakadan da Amurkan zata janye daga India ba.
Rikici tsakanin kasashen biyu ya taso bayanda ‘Yansanda birnin New York suka kama kuma suka yi wa wata mukaddashiyar jakada a karamin ofishin jakadancin India dake New York Devyani khobragade, binciken kwakwab. Ranar Alhamis masu gabatar da kara a Amurka sun ce gungun mutane masu taya alkali yanke hukunci sun tuhumi Devynai da laifin kin biyar ‘yar gidanta karamin albashi da doka ta kayyade, sannan ta shirga kariya a takardar visar kawo ‘yar gidanta din daga India.
A wani matakin sassauta batun Amurka ta bari aka karawa Devyani kariyar difilomasiyya lamarin da ya bata damar barin Amurka.
Jiya jumma’a Khobragade ta isa India, in data godewa kasarta saboda goyon baya da Indiyan ta bada yayin wannan rikici.