Za A Fara Gudanar Da Jana’izar Jimmy Carter A Birnin Washington D.C

Former President Jimmy Carter - funeral

Shugaba Jimmy Carter ya mutu a ranar 29 ga watan Disamban da ya gabata yana da shekaru 100.

An tsara cewa a yau Talata ne gawar tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter za ta isa birnin Washington D.C, inda za’a gudanar da bikin karrama shi a majalisar dokokin kasar gabanin baje kolinta domin baiwa jama’a damar yin ban kwana da ita har zuwa safiyar ranar Alhamis.

Akwatin gawar da ke dauke da shugaban Amurka na 39 zai bar Cibiyar Shugaba Carter da ke jihar Atlanta, inda a karshen makon da ya gabata masu makoki suka yi ban kwana da ita, daga nan kuma za’a tafi da shi zuwa filin jirgin saman sojoji na Dobbins sannan a dora shi a jirgin saman soji na musamman zuwa barikin sojin hadin gwiwa na Andrews.

Akwatin gawar Carter zai bar barikin ta Andrews zuwa cibiyar tunawa da sojin ruwan Amurka, inda za’a karrama gudunmowar da ya bayar a matsayinsa na hafsa mai mukamin laftanal da ya yi aiki a bangaren jiragen karkashin teku masu dauke da makaman nukiliya, kana daga bisani ayarin keken doki ya ja shi zuwa ginin Majalisar Dokokin kasar ta Capitol.

An tsara cewar mambobin majalisar za su fara gudanar da addu’o’i a Capitol da misalin karfe 4.30 na yamma, inda jikokin Carter za su kasance masu rakiyar gawa na musamman.

An kuma shirya cewa Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris da shugaban ‘yan republican masu rinjaye a majalisar dattawa John Thune da Kakakin Majalisar Wakilai Mike Johnson za su gabatar da jawaban karrama mamacin tare da dora furannin kallo akan akwatin gawarsa.

Shugaba Jimmy Carter ya mutu a ranar 29 ga watan Disamban da ya gabata yana da shekaru 100.