Shugaban Kwamitin wasannin Olympics na duniya da ake kira IOC a takaice ya ce "ya na da matukar kwarin gwiwa" za a ba 'yan kallo damar halartar wasannin Olympics da za a yi a Tokyo, wanda aka dage zuwa shekarar 2021, idan har suka samu riga kafin cutar COVID-19.
Shugaban kwamitin na IOC Thomas Bach, ya yi wannan alkawarin ne ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba a babban birnin Japan bayan ganawa da Firai Minista Yoshihide Suga tsawon kwanaki biyu don tattaunawa kan matakan da masu karbar bakuncin wasannin suka tanada.
Bach ya ce kwamitin IOC "zai himmatu sosai" don tabbatar da cewa an yi wa dukkan mahalarta wasannin Olympics allurar rigakafin kafin su isa Japan a watan Yulin da ke tafe idan aka samu riga kafin cutar a lokacin, ta yadda 'yan kallo za su sami "yanayin da zai kare lafiyarsu."
Tun da farko an shirya gudanar da wasannin Olympics na Tokyo ne a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta na shekarar 2020, amma masu shirya gasar da Firai Ministan Japan na wancan lokacin Shinzo Abe suka yanke shawarar dage gasar har tsawon shekara guda a lokacin da cutar COVID-19 ta fara yaduwa a duniya.