Za a ajiye gawar tsohon shugaban kasar Amurka George H.W. Bush a zauren majalisar dokoki Amurka daga yau Litinin da yamma domin ba Amurkawa damar karrama shugaban kasar Amurkan na arba’in da daya.
WASHINGTON D.C. —
Za a bada dama ga manyan baki da kuma jama’a su shiga majalisar domin karrama tsohoun shugaban kasar har zuwa ranar Laraba da safe. Masu sha’awa zasu iya wucewa gaban akwatin da aka ajiye tsohon shugaban Bush, wanda ya rasu a jiharshi Texas, yana da shekaru casa’in da hudu a duniya, bayan ya shafe shekaru yana fama da rashin lafiya.
Bush ya yi mulki wa’adi daya, daga shekara ta dubu da dari tara da tamanin da tara zuwa dubu da dari tara da casa’in da uku. Za a yi addu’oin jana’izarshi a babbar majami’a ta kasa dake nan birnin Washington, daga nan a binneshi ranar alhamis a dakin bincike na shugaban kasa dake Texas.
Ranar asabar fadar White House ta sanar da cewa, shugaba Donald Trump zai halarci jana’izar.