Yunwa Tana Kara Ta'azzara A Zimbabwe

Fari a Zimbabwe

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tace tsananin karancin abinci da ake fama da shi a Zimbabwe yanzu ya kai ga bukatar agajin gaggawa. Tace yawancin al’umman kasar basu samun abinci saboda yawan sauyin yanayi da ya janyo fari da kuma durkushewar tattalin arziki da kasar ke huskanta.

Wata mace mai suna Plaxedes Chibura dake zaune a garin Epworth mai fama da tsananin talauci mai nesan tafiyar awa daya a mota daga kudu masu gabashin babban birnin kasar Harare, tace tana shan wahala matuka kafin ta samu abin da zata ciyar da jikokinta.

hukumomin kai taimako na MDD da gwamnatin kasar sun ce Zimbabwe na buakatar kimanin dala miliyan 218 domin yakar yunwa da ta addabi kimanin mutane miliyan biyar da dubu dari biyar daga yanzu zuwa cikin watan Afrilun 2020.

A don haka MDD tayi kira ga manoman kasar da zuba jari a cikin noman rani da gonar hatsi domin samar da isasshen abinci a cikin kasar.