A karshen taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, Gwamnonin jihohin tafkin Chadi sun bada sanarwar kafa wata gidauniya.
Kafa wannan gidauniyar dai don tattara kudaden da za a yi amfani da su ne wajen farfado da harkoki a yankunan da rikicin Boko Haram ya afkawa.
Wakilin gwamnan yankin Arewa mai nisa na kasar Cameroun ne ya gabatar da sanarwar karshen taron gwamnonin jihohin yankin tafkin Chadi, da ya gudana a ranakun Laraba 17 da Alhamis 18 ga watan Yuli a birnin Yamai.
A ci gaba da neman hanyoyin da za a samu nasarar murkushe Boko Haram ne, ya sa gwamnonin suka kafa wata gidauniya mai suna FSR, domin tattara kudaden da ake bukata don share hawayen al’umomin jihohinsu, inji gwamnan Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum.
Tuni wasu kasashen yammacin Duniya suka fara bada tasu gudunmawar kudade, wasu kuma suka yi alkawarin bayarwa a nan gaba, wanda hakan ya karawa jagororin wannan yanki kwarin gwiwa, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Yobe Baba Malan Wali ya shaida wa wakilin Muryar Amurka.
Gwamnonin wadannan jihohi kimanin 8 sun jaddada aniyar ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu, don yunkurin samar da ci gaban da ake fatan samarwa ga al’ummomin dake zaune a yankin tafkin Chadi, shi yasa kasar Cameroun ta amince ta karbi bakoncin irin wannan haduwa a shekara ta 2020.
Gwamnan Diffa Mohamed Moudour ne aka zaba domin shugabancin kungiyar wadannan gwamnonin, kuma a cewar shugaban majalisar mashawartar karkara ta Diffa Mahirou Ligari, za a ga aiki da cikawa.
Taron na birnin Yamai ya dau alwashin ganin sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kungiyoyin fararen hula, da na mata, matasa na da rawar takawa a wannan yunkuri.
Saboda haka aka yanke shawarar basu cikakken matsayi wajen dukkan shawarwarin da aka tsayar a lokacin wannan haduwar.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti.
Facebook Forum