Hukumar lafiya ta duniya ta WHO, ta ce barkewar annobar Ebola a jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, “matsalar lafiyar al’umma ce ta gaggawa da ta zama abin damuwa ga kasashe.
Hukumar ta ce mutanen farko da suka kamu da cutar Ebola a garin Goma, daya daga cikin manyan biranen kasar, ne suka sa aka ayyana dokar ta baci.
Hukumar ta WHO ta kuma bayyana yaduwar cutar a matsayin “abin damuwa, inda ake samun rahoton mutane 10 zuwa 15 dake kamuwa da cutar a kowacce rana, kuma mutane 1,676 sun mutu tun bayan da annobar ta barke, Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban daraktan hukumar ta WHO ya shaida hakan.
Sai ya kara da cewar “Binciken mu akan hadarin dake tattare da yaduwar cutar a jamhuriyar dimokradiyyar Congo da kuma yankin har yanzu yana da yawa, amma hadarin bazuwar cutar a wajen yankin bai da yawa."
Facebook Forum