Idan kuma ta gaza daukar matakan da suka dace, akwai yiwuwar kasar za ta dada shiga matsalolin da ka iya rikidewa zuwa tarzoma.
Masana na kara jaddada mahimmancin gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen kawo karshen matsalolin tsadar rayuwa, yunwa da talauci da masu bibiyar al’amurra suka ce baya rasa nasaba da cire tallafin man fetur a daidai lokacin da farashin kayayyakin abinci ke kara tashi a kasuwanni, suna masu cewa dole ne a kaiwa al’umma dauki cikin gaggawa.
A game da sabon salon fasa rumbunan ajiyar kayayyakin abinci na gwamnati da ‘yan kasuwa ko tare tituna don abka wa motocin dakon kayayyakin abinci, mun tuntubi shugaban tsangayar koyar da aikin lauya a jami’ar Nile da ke Abuja kuma masani a fannin shar’ia, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, a kan wannan dabi’ar inda ya ce tarihin kowane dan adam ya fara ne daga cikinsa kuma gwamnati ta san irin matakan da ya kamata ta dauka wajen kawo sauki a cikin yanayin da ake ciki.
Ita ma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Faiza Nasir ta bayyana cewa za a iya danganta fasa rumbunan ajiye abinci da abubuwa biyu wato a wani bangare yunwa, wani kuma mugunta.
A cewar masanin siyasa, Abubakar Muhammad Abu Jega, talauci babu abun da yunwa baya sawa, yana mai cewa idan har gwamnati ta bar al’ummar ta cikin talauci to al'amarin zai iya rikidewa zuwa abun da ba a zato.
A bangararen jihohi kuwa, gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce magance matsalar tsaro na daga cikin matakan da za su kawo sauki a cikin yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya.
Idan ana iya tunawa, daga kasa da makonnin biyu da suka gabata an fuskanci yadda wasu matasa suka abka wa motocin dakon kayayyakin abinci a wani yankin jihar Neja da wasu wurare, kuma da safiyar ranar lahadi ne wasu matasa suka abka wa wani rumbun ajiye kayayyaki abincin mahukuntan babban birnin tarayyar kasar, lamarin da ya kai ga kamen wasu mutane 15 da ake ganin suna da alaka da wannan danyen aikin.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake fashe-fashen rumbunan abinci, ko a lokacin kullen annobar korona birus an fasa wurare da dama sakamakon yunwa da aka yi fama da ita a wancan lokaci sakamakon dokar zaman gida da ta hana mutane neman na tuwo kamar yadda suka saba a yau da kullum.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5