A wani bangare na tsara kawo karshen wannan matsala, kasashen dai tuni sun amince kan ware wasu makurden kudade da za’ayi wannan aiki da shi, sai dai kuma masana na ganin harhada kudin na iya zama damuwa. A cewar tsohon babban sakataren hukumar raya kofin Neja mai kasashe tara Alhaji Baba Ba’aba ‘dan masanin Fika yace dole Najeriya tazama uwa da makarbiya wajen karbar wadannan kudade.
A wani yunkurin yiwa ‘yan kungiyar Boko Haram kwab ‘daya tuni shugaba Muhammadu Buhari ya mayarda cibiyar bada umarnin yaki da ta’addanci zuwa garin Maiduguri fadar jihar Borno.
Duk da cewar an kirkiro runduna ta bakwai mai mazauni a Maiduguri, yanzu kuma ankai wannan cibiya ta bada umarnin yaki da ta’addanci, anya kuwa baza’a samu karo da juna ba wajen kudanar da wannan yaki? Masani akan harkar tsaro Dakta Mohammed El-nur Dongin yace, gaba ‘dayan su bazasuyi wani abu ba sai sun sami umarni daga cibiyar, hakan zai tamaka wajen rage wahalar tafiya da akeyi a baya na zuwa Abuja. Dakta ya kara da cewa wannan zaiyi tasiri kwarai da gaske domin shugaban kasa ya nuna shine babban abinda ya dameshi a yanzu cin galabar yakin shine zai taimakawa sauran batutuwan kasa suyi sauki.
Saurari rahotan
Your browser doesn’t support HTML5