Wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce an kama jagoran yinkurin juyin mulkin Lutanal Kelly Ondo Obiang, wanda kuma ya ayyana kansa a zaman shugaban abinda su ka kira, Kungiyar Yan kishin Kasa da Kare Jami’an Tsaron Gabon.
Obiang ya kasance na karshen da aka kama cikin gungun manyan sojoji biyar da aka kama a jiya Litinin. Sojojin gwamnati sun kashe wasu sojoji biyu masu nasaba da yinkurin juyin mulkin.
Mai magana da yawun gwamanatin Gabon Guy-Bertrand Mapangou, yace an shawo kan al’amarin zuwa yammacin jiya Litinin, kuma gwamanati ta sake kwace gidajen rediyon gwamnati da kuma wata babbar hanya mai hada wasu muhimman wurare a Libreville, babban birnin kasar, wanda dama wurare biyu ne kadai masu yunkurin juyin mulkin su ka kama.