‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga a babban birnin kasar Sudan a jiya Lahadi, yayin da zanga-zangar kira shugaba Omar al-Bashir ya sauka daga mulki take shiga mako na uku.
Masu zanga-zangar sun taru a birnin Khartoum a jiya Lahadi, suna sauraren kungiyar kwararrun ma’aikata ta Sudan, kungiyar da ta hada da likitoci da malamai da injiniyoyi da suka ayyana yajin aiki da zanga-zanga tun a cikin watan da ya gabata.
‘Yan sandan sun mai da martani a kan masu zanga-zangar ne da barkonon tsohuwa domin su tarwatsasu. Wasu hotunan bidiyo da aka dora a kan yanar gizo sun nuna masu fafutukar kin jinin gwamnati suna nunawa mutane hanya suna arcewa a kan manyan hanyoyin domin kaucewa hayakin mai sa hawaye.
Gwamnatin Sudan tace, mutane 19 ne aka kashe, ciki har da jami’an tsaro guda biyu, tun lokacin da aka fara zanga-zangar a birnin Atbara dake arewa maso gabashin kasar a ranar 19 ga watan Disamba.
Ita kuwa kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce mutane 37 aka kashe a cikin masu zanga-zangar.
Facebook Forum