Yanzu haka dai babban Bankin Najeriya yana ci gaba da fitar da miliyoyin Daloli zuwa kasuwar hada-hadar kudade, inda a wannan makon ya sako Dala miliyan 367 don cimma bukatun ‘yan kasar.
A makon da ya gabata ma sai da babban Bankin ya sako Dala miliyan 180 ranar Litinin da kuma karin wasu miliyoyi har 350 a ranar Juma’a, don baiwa Naira damar samun daraja a fadin kasar.
Daraktan hulda da jama’a na babban bankin Najeriya, Dakta Isaac Okorafo, yace a duk lokacin da suka saki daloli masu yawa Naira na ‘kara samun daraja.
A cewar Dakta Isaac, akwai masu son shigo da kayayyakin ababen sarrafa masana’antu da kuma na’urori da wadanda kuma ke bukatar canjin domin biyan kudaden makaranta ko zuwa jinya asibiti ko kuma guzuri na asibiti.
Wandanda ke son shigar da kayayyaki na masana’antu sune aka baiwa sune aka baiwa Dala miliyan 367 yayin da wadanda ke son zuwa jinya ko makaranta aka basu Dala miliyan 50.
An dai bukaci Bankunan Najeriya da su rika tabbatar da ganin sun canzawa mutane kudaden, duk wani ‘dan Najeriyar da ya nemi canjin bai samu ba a cikin awa 24 to ya kai ‘karar Bankin zuwa babban Bankin Najeriya domin a dauki mataki akai, inji daraktan hulda da jama’a na babban Bankin Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5