Farfasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa kaddamar da layin dogo na zamani na daya daga cikin alkawuran da Shugaba Muhammad Buhari ya yiwa 'yan Najeriya yayinda yake fafutikar neman zabe da ya maimaita ranar da aka rantsar dashi, kuma shi ne shugaban ya fi baiwa fifiko.
Nufin shugaban Najeriya ne ya gani cewa an hade akasarin jihohin Najeriya da layin dogo ta yadda za'a samu sukunin fitar da kayan gona na yau da kullum daga Najeriya zuwa kasashen waje kana daga kasashen wajen zuwa cikin lungunan kasar.
Injiniya Usman Abubakar shugaban gudanarwa na hukumar jiragen kasan Najeriya yace gina layin dogo na zamani ba karamin alheri ne ya samu Najeriya ba saboda duk duniya an koma daukan kaya ta hanyar layin dogo. Yace abun da aka yi shi ne mataki na farko na hade kasar gaba daya da layin dogo. Bayan wannan ya tsaya a Ibadan za'a cigaba dashi har zuwa Kano. Ya bada misali da sabon layin dogon da ya hada Kaduna da Abuja da yanzu mutane ke jin dadinsa.
Shirin gina layin dogo zai hade babbar tashar jiragen ruwa da duk sassan Najeriya.
Shugabar hukumar tasoshin riragen ruwan Najeriya Hajiya Hadiza Bala Usman tace idan ba'a hada tashar jiragen ruwa da layin dogo ba da zai dinga kawashe kaya babu yadda arewa zata anafana. Layin dogo zai taimaka da kai kaya koina da kuma kwaso kayan zuwa tashar jirgin ruwa idan za'a fitar dashi.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum