A cikin `yan kwanakin nan ne aka kai hari kan `yan Najeriya a kasar ta Afirka Ta Kudu, inda aka kona musu dukiya mai dinbin yawa.
Majalisar Wakilan dai ta yanke shawarar tura wata tawagarta ne domin su gana da takwarorinsu dake a Afirka ta Kudu, da nufin gano hanyar magance kyamar da ake nunawa baki musamman ma ‘yan Najeriya.
Tawagar ‘yan Majalisar da suka hada da ‘yan kwamitin da ke kula da harkokin kasashen waje da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje. ‘yan Majalisar dai sunce lokacin yayi da ya kamata a kawo karshen kuntatawa ‘yan kasar mazauna Afirka ta Kudu, kuma aikinsu ne su nunawa duniya ‘yan Najeriya suna da gata.
Yayin da ‘yan Majalisar ke fafutukar kare muradun ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu, masana harkokin diplomasiyya na ganin ba laifi bane, amma dai suna ganin idan gwamnatocin kasashen biyu zasu fuskanci lamarin sosai da za a fi samun biyan bukata.
Domin karin bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka.
Facebook Forum