Yudala Zai Fara Amfani Da Jirage Maras Matuki

This undated handout photo released by Amazon on December 1, 2013 shows a flying "octocopter" mini-drone that would be used to fly small packages to consumers. Amazon CEO Jeff Bezos revealed on December 1 that his company was looking to the future with pl

Kamfanin Yudala dake sayar da kayyakin sadarwa na zamani ta kan yanar gizo a Najeriya, ya fitar da sanarwar zai fara amfani da jirage maras matuki da ake kira drones a turance don su gaggauta isar da hajoji ga abokan cikini.

Kamar yadda rahotanni ke nuni, kamfanin dake akan yanar gizo ya shirya yin amfanin da jiragen maras matuki, amma yana jiran a bashi izini tukunna daga hukumomin da suka kamata kafin fara amfani da su.

Alokacin da shugaban kamfanin Prince Nnamdi Ekeh ke magana da gidan jaridar Nation Newspaper, yace “mun riga mun samu jirgen da zamuyi amfani da su daga wani kamfani a Asia, domin rage bata lokaci da cunkoson motoci ke haddasawa a manyan birane a Najeriya. Muna aikin neman izini da ya dace domin yin haka daga hukumomin gwamnati da suka kamata.”

Ya kuma ci gaba da cewa nan ba da dadewa ba kamfanin mu zai cimma wani buri a fannin kasuwanci ta kan yanar gizo.

Kamfanin Yudala dai ya hada kai da wasu manyan kamfanonin da ke kera kayayyakin fasaha na zamani da suka hada da Microsoft da INNJOO da Infinix da Sony da Apple da HP da dai sauransu, domin baiwa abokan cinikayyar su zabi kan duk kayan da suke so, dama baiwa abokan cikin taimakon kan hajojin da suka saya.

Da zarar sun sami izinin amfani da jiragen, to kamfanin Yudala zai zama kamfani na farko da ya fara amfani da irin wannna fasaha wajen dakon kaya ga abokan ciniki a Najeriya, yanzu dai mutane na jira don ganin yadda zata kasance.