Kamfani Apple ya fito da wasu sabbin kayayyaki da suka hada da akwatin Talibijin, da sabuwar wayar Apple 6S da kuma wata karamar na'urar Tablet.
Sabbin wayoyin na kamfanin Apple mai suna iphone 6S da 6S plus, wanda ya kasance wayar da ta fi kawo wa kamfanin Apple kudi, girman ta 'daya ne da ta farko sai dai ita tazo ne da sabuwar kamarar daukar hoto wanda tafi ta wayar baya, kai kwakwalwar wayar ma tafi girma wanda tafi sauri, bugu da kari kuma an samar da sabbin launuka da wani nau’in “3D Touch”.
Da yake jawabi a gaban dubban mutane da suka hada da masu sharhi da ‘yan jarida da kuma ma’aikatan kamfanin na Apple, shugaban Kamfanin na Apple, Tim Cook, da wani jami’in, kamfanin Microsoft da ya rufa masa baya ya bada misali kan abubuwan da sabuwar kwanfutar hannun ta kamfanin na Apple, wato Ipad ke iya yi.
A bikin nunin talabijin din na Apple, an nuna wasu dabaru da aka cusa a cikin sabuwar talibijin din domin tabbatar da saukin sarrafawa da kuma iya yin gaba ko kuma baya a lokaci da mutun ke kallo da kuma iya sarrafa ta da murya.