Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Milliyoyi Na Iya Samun Aiki Ta Shafin Zumuntar Facebook


Facebook
Facebook

A satin da ya gabata ne, shafin zumunta na Facebook, ya samu karin sababbin mutane, da suka bude shafufuka na zumunta, da suka kai yawan mutane Billiyan daya a rana daya.

Wannan ya jawo hankalin kamfanoni masu neman ma’aikata, sun karkata don bayyanar da wasu gurabe da suke da bukatar daukan ma’aikata, masu can-can ta a gurabe da dama.

Ba wai kawai yawan masu ma’amala da wannan shafin zumuntar ne, kawai yasa yazamo abun daukan hankali, ga masu neman ma’aikata da bincike ba.

A kwai tabbacin cewar kimanin kashi saba’in 70% na mutane da suke da shafin zumunta na facebook, na ziyartar shafin a kowace rana, don sanin abun da ke wakana a wasu sassan duniya.

Wannan ya nuna cewar, yafi yawan kashi goma sha uku 13% na mutane da ke da shafin zumunta na LinkedIn, wanda aka kirkire shi don tallata kai, da kwarewa a wasu fannoni na aiki da bayyanar da, abun da mutun yasani kuma zai kai wa kamfani idan suka dauke shi aiki.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2015, ya bayyanar da cewar. Mafi akasarin mutane masu neman aiki, sun dauki cewar shafin Linkedin, shine shafi da yafi can-can ta ace sun bude shafi, sabo da zaman shi shafin kwararru a sana’a. Suma masu neman ma’aikata sukan je wannan shafin ne kawai don tsamo ma’aikata kwararru.

A cewar wani kamfani na daukar ma’aikata, mai suna Jobvite, sun bayyanar da wani rahoto, da yayi nuni da cewar, kimanin kashi sittin da shida 66% na matasa da suka samu aiki a kamfanin, sun zakulo su ne daga shafin facebook.

Idan har dai kana ko kina, sa ran zaku zama masu neman aiki nan kusa, to lallai akwai bukatar matasa su san me suke rubutawa a shafin su na facebook, da kuma yadda suke mu’amala da abokan su a fadin duniya, domin kuwa baku san irin mutanen da zaku hadu da suba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG