Matan sun fadawa 'yan sanda cewa sun shirya wani wasan kwaikwayo domin su wayar da mutane a illolin safarar bil adama, suka ce nan yan bindigan suka tada wasan kuma suka yi garkuwa dasu.
Wani jami’in dan sanda yace matan suna yiwa wata kungiya mai zaman kanta ta Asha Kiran wacce ke samun taimako wata kungiyar addinin Krista na yankin.
Yan sandan sun ce suna zaton magoya bayan Pathalgadi ne suka aikata wannan danyen aikin. Su magoya bayan Pathalgadi dai basu son bako a cikin yankinsu.
Fitilar duniya tana haskawa a kan dabi’ar fyade da ya kunno kai a India a shekarar 2012 inda tarin mazaje suka yiwa wata mace fyade kuma suka kashe ta a cikin motar bos a birnin New Delhi, lamarin da ya tada fushin wasu masu zanga zanga.
A shekarar 2016, an yiwa mata dabu dari hudu fyade a India, wanda ya kai kashi 60 cikin dari a kan 2012. Kusan kashi 40 cikin dari na wadanda aka yiwa fyaden kananan yara ne.