Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran aikinsa na Ukraine Petro Poroshenko sun tattauna kan batun aiwatar da 'yarjajjeniyar zaman lafiya ta 2015 wadda ta kasa kawo karshen tashin hankali a gabashin Ukraine, a cewar jaridun kasar ta Rasha.
"Putin ya bayyana damuwa kan karuwar tashin hankali a Donbas da kuma farar hula da dada shiga uku saboda yawan hare-haren da sojojin Ukarain ke kaiwa a yankin," a cewar fadar Kremlin.
A cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a Minsk a watan Fabrairun 2015 to amma tashin hankali na dada cigaba a yankin, inda mayakan bangarorin biyu su ka saba da yarjajjeniyar tsagaita wutar kulluyaumin.
Shugabannin biyu sun yi magana ta wayar tarho jiya Alhamis, wadda ita ce tattaunawarsu ta biyu cikin makonni biyu da su ka gabata, a cewar kafar labarai ta Rasha, Interfax. Kamfanin dillancin labaran ya ce Poroshenko ya kira Putin ranar 9 ga watan Yuni don su tattauna kan batutuwan jinkai, ciki har da musayar fursuna.
Facebook Forum