Yin Sana’ar Wankin Takalma Don Gujewa Bara

Almajiri mai sana'ar wanke takalma

A dalilin kaucewa maula da dogaro da kai ne wani almajiri mai suna Abubukar Sadiq, wanda yake sana’ar wanke takalma (shoe shiner), ya fara wannan sana’a ne domin kaucewa bara da roko kuma yakai watanni kamar uku da fara wannan sana’ar tasa.

Abubakar Sadiq ‘dan asalin Katsina yaje birnin Kano ne domin karatun allo, amma don kada yayi bara shine yasa ya fara wannan sana’ar kuma bata hanashi yin karatun sa, yana tafiya wankin takalmi ne ranar Alhamis da Juma’a ranakun hutun makaranta su kuma ranakun dayake zuwa makaranta kuwa yana tafiya sana’ar sa bayan an tashi daga karatu.

Yana amfani da kudin daya samu domin taikamawa kansa wajen sayen sutara, abinci, da sauran kayan amfanin yau da kullum, Abubakar dai na fatan samun sana’ar da tafi wanke takalma a gaba don samun hanyar dogaro da kai.