Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Kayata Sana'a Itace Hanyar Saidawa ba Yawan Jariba


Sana'a
Sana'a

Hajiya Gaje Na-Sidi, shugaban kungiya me yunkurin tallafawa mata don bunkasa sana’o’in su da kuma tallafamusu wajen samun jari a jihar Kano. Tayi bayyanar da manufofin kungiyar su, da cewar ba wai samar da kudin ga mata ne abun da suka sa a gababa, sunma fi maida hankali a wajen yadda zasu tallata musu da hajar su don bunkasar kasuwancin.

Ganin cewar yanzu an cigaba a duniya, idan har kana sana’a, baka zamanantar da itaba to lallai wannan sana’ar tana iya samun koma baya, don haka mutane su maida hankali wajen tsafftace sana’ar su da kuma samar da kyawawan mazubi don kayatar da haja.

Kuma duk mace da ta samu wanna tallafin zasu iya samu jari daga naira miliyan daya zuwa miliyan biyar, wanda kuma za’a bukaci da su maida uwar kudin a cikin shekara daya.

Ta bakin Hajiya Yahanasu Tarauni, lallai suna dagacin wadanda suke saran cin gajiyar wannan tsari na kungiyar, kuma suna saran wannan kungiyar zata tallata musu hajar su bayaga basu kudin, don mafi akasarin lokkuta ba wai jari ne matsalar suba, yadda zasu saida hajar ta su itace babbar matsala. Amma da wannan shirin ganin an kara wayar musu da kansu ta yadda zasu gyara, su sa a cikin mazubi mai kayatarwa lallai wannan zai taimaka matuka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG