Wani janar a rundunar sojojin Burundi yace ya hambarar da shugaba Pierre Nkurunziza, wanda a yanzu haka ba ya kasar yana halartar taron kasashen yankin gabashin Afirka.
Janar Godefroid Niyombare shi ya bayarda wannan sanarwa yau laraba ta gidajen rediyo da dama masu zaman kansu.
Wakilin Muryar Amurka, Gabe Joselow, wanda yake Bujumbura, babban birnin Burundi a yanzu haka, yace babu tabbas a kan ko shi Janar din yana samun goyon bayan dukkan rundunar sojojin kasar.
Joselow yace an yini a yau ana ta harbe-harbe a birnin a yayin da 'yan sanda ke arangama da masu zanga-zanga.
Wannan yunkurin juyin mulkin ya biyo bayan makonnin da aka shafe ana tankiya a kan shirin shugaba Nkurunziza na yin Tazarce.
Masu sukar lamirin wannan yunkuri sun ce yin wa'adi na uku a kan karagar mulki ya sabawa tsarin mulki, yayin da magoya bayan shugaban suke cewa ai wa'adinsa na farko da ya fara a 2005, majalisar dokoki ce ta zabe shi ba ta hanyar zabe na kasa ba.