Yin Ban Kwana Da Gwarzon Dambe Mohammed Ali

Mutane na yin ban kwana da Mohammed Ali

Dubun dubatar mutane ne ake sa ran za su jeru a gefen titunan garin Musulmin farko da ya fi shahara a Amurka, domin yin ban kwana da gwarzon dambe Muhammadi Ali, wanda ya rasu a ranar juma’ar da ta gabata yana mai shekaru 74.

Ana sa ran jerin gwanon motocin da zai tafi da gawar Muhammad Ali zai dauki minti 90 yana tafiyar kilomita 37 a cikin birnin Louisville da ke Kenturkey.

Jerin gwanon zai faro ne daga wuraren da suka kasance muhimmai ga marigayin, inda zai ‘kare a makabartar Cave Hill da za a binne shi.

Daga cikin wadanda za su taimaka wajen raka gawar ta Muhammad Ali akwai tsohon zakaran dambe Lennox Lewis da dan wasan kwaikwayon nan da ya fito a matsayin Muhammad Ali a wani fim da aka shirya domin nuna rayuwar marigayin, fim din da har ila yau ya samu shiga jerin fina-finan da aka ware domin karbar kyautar karrama jarumai ta Oscar.

Za kuma a yi wani taron tunawa da mamacin a filin wasa na Lousville da mislin karfe biyu na rana, inda tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da dan wasan barkwanci Billy Crystal za su gabatar da jawaban tunawa da Muhammad Ali.