Dakarun Tabbatar da zaman Lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka da ke Somaliay sun ce sun kashe sama da mutane 100 na mayakan Al-Shabab, wadanda su ka kai hari a wani sansanin soji a yau dinnan Alhamis.
Jami'ai da kuma mazauna wurin sun ce 'yan bindigar sun tayar da bam cikin wata mota sannnan su ka yi yinkurin abkawa cikin sannan sojojin Habasha a kauyan Halgan, mai tazarar kilomita 260 arewa da birnin Mogadihsu.
Kanar Joseph Kibet, mai magana da sojojin AU na AMISON, ya gaya ma Shashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa sojojin Habasha da Somaliya sun fattaki wadanda su ka kai harin na asuba. "Rahoton farko na nuna cewa an kashe mayakan sama da 110 a wannan harin," a cewarsa.
Ma'aikatar Harkookin Wajen Somaliya ta ce mayakan da aka kashe sun kai akalla 120.
Shugaban kauyen, Guhad Abdi Warsame, ya gaya ma Muryar Amurka cewa Al-Shabab sun kai hare-hare biyu, daya ya auna wani rukunin gidajen da sojojin Habasha ke ciki, dayan kuma sansanin sojojin Somaliya. Ya ce baba harin da ya yi nasara kuma gwawarwakin maharan na nan yashe a kauyen.