Zakarar damben, wanda dubban miliyoyin jama'a suka sani a fadin duniya, ya rasu ne makon jiya yana da shekaru 74 bayan shekaru yana fama da cutar makyerketa ko Perkinsons da turanci.
Anyi addu'o'in ne a wurin da Muhammed Ali yayi dambensa na farko a garin da aka haifeshi a shekarar 1960, jim kadan bayan da ya sami lambar zinari a gasar Olympic da aka yi a Roma.
Musulmai da masu karrama shi duk suka ce Muhammed Ali shine "alamar muslunci" mutumin da yake karfafa zaman lafiya da mutunta mabiya wasu addinan.
Yau Jumma'a za'a yi masa wasu addu'o'i na musamman a zaman hadin guiwa na mabiya addinai daban daban a birnin na Lousiville dake jihar ta Kentucky.