Fadar shugaban kasar Najeriya ta Aso Rock a Abuja, ta ce yin afuwa ga mayakan Boko Haram zai amfani kasar ta fuskoki da dama.
Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, mai bai wa shugaba Buhari shawara a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shirin afuwar zai iya sa mayakan su ajiye makamansu.
Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen rage yawan kudaden da ake kashewa domin samar da tsaro da kuma rayukan da ake asara.
A baya gwamnatin ta Najeriya, ta taba ta da wannan batu na afuwa amma kuma lamarin bai yi wu ba.
Akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Najeriya kan a yi wa mayakan na Boko Haram afuwa ko kuma akasin hakan.
Gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua ta taba yi wa kungiyoyin tsagerun yankin Niger Delta afuwa, domin su ajiye makamansu.
Rikicin Boko Haram ya faro ne tun daga 2009, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyin da muhallansu a wasu kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.