Rundunan tsaron farin kaya ta Sibil defens, NSCDC, a Najeriya tace abun takaici ne irin tashe tashen hankulan dake faruwa a jihar Taraba,musamman a tsakanin makiyaya da manoma lamarin dake jawo asarar rayuka da dukiya.
Domin tabbatar da kare rayuka da ma dukiyar ne yasa rundunan tsaron raba manyan babura ga jami’an ta da aka tura tsaunin na Mambilla,don kai dauki cikin gaggawa a yankunan da ake samun tashe tashen hankula.
Tun farko da yake mika wadannan manyan baburan kwamandan rundunan a jihar Taraba Kamilu Isa Ado,wanda shi ya wakilci babban kwamandan a Najeriya,Abdullahi Gana Muhammad,ya gargadi jami’an ta sibil defens da su yi aiki tsakaninsu da Allah,don tabbatar da samun zaman lafiya a yankin na Mambilla dake fama da tashe tashen hankula.
Shima da yake bayyana jin dadinsu,Mukaddashin shugaban karamar hukumar Sardauna, Rabaran Godwin Sol,ya yaba da kokarin da ya ce jami’an tsaro na yi a yanzu,domin maido da zaman lafiya a yankin,kana kuma ya bukaci sauran hukumomin tsaro da su yi koyi da hukumar ta sibil defens wajen baiwa jami’an su kayain aiki,don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Wannan ma ko na zuwa ne yayin da babban kwamandan rundunan tsaron ta sibil defens a Najeriya Abdullahi Gana Muhammad ke rangandin wasu jihohin arewa maso gabas,game da batun fadar makiyaya da manoma,da kuma batun tabbatar da tsaro a makarantu domin kare rayukan dalibai daga hare haren yan bindiga masu tada kayar baya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum