Yaya Jammeh Yace Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa

Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya

Shugaban na Gambiya yace jama'a zasu sake zaben sa bisa hujjar ayyukan da yayi a tsawon shekaru 17 da yayi yana mulkin kasar.

Shugaban kasar Gambia Yahaya Jammeh yace yana da kwarin guiwa, zai samu wani sabon wa’adin mulkin shekaru biyar a zaben shugaban kasar da aka yi wanda kungiyar bunkasar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta yi tur da Allah waddai da shi.

Mr.Jammeh ya shaidawa manema labarai cewa jama’a za ta sake zaben shi bisa hujjar ayyukan da yayi a tsawon shekaru 17 da yayi yana mulkin kasar tun hawan shi cikin wani juyin mulki. Shugaban yace ya yi ayyukan ci gaban kasa fiye da yadda Birtaniya ta yi a cikin shekaru 400 da tayi tana yiwa kasar mulkin mallaka.

Magoya bayan shugaban kasar sun ce ya taimaka wajen kyautata ababen more rayuwa da tsarin ilimi da kuma kula da lafiya. Amma masu sukan lamirin shugaban sunce har yanzu kasar Gambia tana fama da tsananin fatara da talauci. Suna zargin cewa da hannun shugaban kasar a cikin kashe-kashe da gana ukuba da hana bakin magana ga bijirarrun siyasa da kuma tauye ‘yancin yada labarai.

Kungiyar bunkasar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta fada a makon jiya cewa ba za a iya cewa an yi zaben cikin gaskiya da adalaci ba, har ma ta ambaci wasu zarge-zargen cewa an yi amfani da matakan razana masu kada kuri’a kuma jam’iyya mai mulki ce ke yin yadda ta ga dama da kafofin yada labarai.