Senegal ta janye jakadanta a Iran,bayan abin fallasa na makamai,da ake zargin suna kan hanyarsu zuwa Gambia.
Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen Senegal jiya Talata tace bata gamsu da bayanan da Iran ta bayar ba.Tace gwamnatin ta janye jakadan nata ne domin tuntuba. Kasashen Sengala da Iran suna kyakyawar dangantaka har zuwa 13 ga watan Okotoba lokacinda aka kama tulin jibgin akwatuna da makamia a tashar ruwa dake Legas.Tehran tace makaman suna kan hanyarsu zuwa wata kasa ce dake yammacin Afirka,wadda daga bisani aka gane cewa Gambia ce.
Kan wan nan Gambia ta yanke huldar jakadanci da Iran.
Masu sharhi a Senegal, sunce sai tayu makaman na wasu ‘yan aware ne dake da tunga a yankin casamance.