Yawan Wadanda Suka Mutu a Ambaliyar Ruwan Brazil Ya Karu

  • Ibrahim Garba

Hoton malalar tabo kenan da aka dauko daga sama a Tresopolis na Brazil

Masu ayyukan ceto a Brazil na kokarin nemo wadanda har yanzu keda rai, bayan ambaliyar ruwa da malalar tabo sun abka ma yankin tudun da ke arewacin birnin Rio de Janeiro, da su ka hallaka kusan mutane 400.

Masu ayyukan ceto a Brazil na kokarin nemo wadanda har yanzu keda rai, bayan ambaliyar ruwa da malalar tabo sun abka ma yankin tudun da ke arewacin birnin Rio de Janeiro, da su ka hallaka kusan mutane 400, su ka kuma raba daruruwan mutane da muhallansu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haddasa wannan hadarin day a yi matukar barna a fadin yankin Serrana da ke kusa da birnin Rio de Janeiro. Gefe-gefen tuddai sun yi ta fadawa bayan ruwa da isaka sun jibga dinbin ruwa mai kimanin yawan ruwan da aka yi mata guda ana yi, kuma masana sun yi gargadin cewa da yiwuwar samin karin ruwan a kwanaki masu zuwa.

A garin Teresopolis, akalla mutane 161 ne aka ce sun mutu, kuma daruruwa su ka rasa muhallansu. Hasalima saida aka maida Majami’u da ofisoshin ‘yan sanda wuraren ajiye gawarwaki.