Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 100 Sun Halaka A Indiya,Wasu 90 Sun Jikkata A Ture-reniya


Mabiya addinin Hindu a wani babban wurin ibadarsu.
Mabiya addinin Hindu a wani babban wurin ibadarsu.

A daren jiya Jumma’a ce gungun masu ibada a India sun kutsa da mota kan wasu takwarorinsu,wanda ya janyo turereniya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 100.

A daren Jumma’a ce gungun masu ibada a India suka kutsa da mota kan wasu takwarorinsu,wanda ya janyo turereniya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 100.Jami’an India suka ce wasu 90 kuma sun jikkata.

An yi hadarin ne a cikin jihar Kerala dake kudanci. Wadanda ke cikin motar suna dawowa ne daga wani bikin addini lokacinda motar Jeep da suke ciki ta kubuce musu ta auka kan taron wasu masu gangamin ibada.

Ahalin yanzu kuma hukumomi a Mexico sunce an kashe ‘yan bangar fataucin miyagun kwayoyi dauke bindigogi su 12 da sojojin kasar biyu, a wani musayar wuta da ya dauki kusan sa’o’I shida,a jihar Velacruz dake kan gaba.

Jami’ai suka ce lamarin ya auku ne a daren Alhamis sa’ilinda jami’an tsaro suka gane wani gida mafakar fataken miyagun kwayoyi a wajajen fitar birnin Xalapa,fadar jihar Velacruz.

Rahotanni sunce an bude wa jami’an tsaro wuta yayind a suka zagaye gidan.

Fiyeda mutane dubu 34 ne suka halaka tun fara yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi cikin fadin kasar a 2006.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG