Bayan an basu horo yau ne za'a rantsar da shugabannin kananan hukumomi da aka zaba a jihar Jigawa
WASHINGTON, DC —
A jihar Jigawa yau za'a ratsar da shugabannin kananan hukumomi ashirin da biyar.
A ranar 18 ga watan jiya ne hukumar zabe ta jihar Jigawa ta gudanar da zaben kananan hukumomi ashirin da bakwai.Jam'iyyar PDP ta lashe kujeru ashirin da biyar yayin da hukumar zaben ta sanarda soke zaben kananan hukumomi biyu wato Hadeija da Malammadori bisa ga dalilai na tsaro.
Alhaji Salisu Sale Indrawa kwamishanan kananan hukumomi na jihar yace ya kamata a sanarda kananan hukumomin da ba za'a rantsar da nasu shugabannin ba domin su gane dalilan da suka sa hakan. Yace sun tara shugabannin kananan hukumomi da kansiloli inda suka jaddada mahimmancin hadin kai domin idan babu hadin kai ba za'a samu cigaba ba.
Kafin a kai ga sa ranar ratsar da wadanda aka zaba sai da aka yi masu bita da fadakarwa kan ayyukansu da kalubale dake gabansu.Mikaila Sabo kansila ne karo na uku yace gaskiya sun koyi abubuwa da yawa. Na farko yace bayan maganar dokoki akwai magana ta dangantaka da wasu da suke aiki da su misali sarakunan gargajiya. Yace an nuna masu dangantakarsu da abokanan aiki da yawa wanda ma basa kusa da juna. Yace duk abun da suke yi domin talakawan da zasu yiwa aiki ne. Shugabanci ya kunshi yadda zasu kare mutanensu da dukiyoyinsu.
Wani sabon shugaban karamar hukuma Alhaji Sale Magaji wanda ya kwashe shekaru hudu yana mataimakin shugaban hukumar tasa yace zai yi anfani da abun da ya sani a karamar hukumar saboda kyakyawar dangantaka dake tsakanisa da wanda ya gada. Da yaddar Allah abubuwa zasu zo masa da sauki. Yace idan mutum zai yi shugabanci ya san amana da hakokin dake kansa.
Ga Mahmud Kwari da cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5