Yau Za A Fara Shari'ar Tsige Tsohon Shugaba Trump Karo Na 2

Yau za'a fara sauraron karar sake tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a majalisar dattawan Amurka.

A yau, Talata za a fara Shari’a mai cike da tarihi, ta tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump, karo na biyu a majalisar dattijan Amurka, inda ake zargi Trump da tunzura, tayar da hankali wata guda da ya gabata ta hanyar ingiza magoya bayansa, da su tunkari ‘yan majalisar a ginin majalisa ta Capitol. Yayin da suke tabbatar da cewa dan jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kayar da Trump a zaben 2020.

Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, yayin da kusan magoya bayan Trump 800 suka afkawa mahukuntan a cikin ginin Majalisar, suka fasa kofofi da tagogi, suka yi wa wasu ofisoshin majalisar kawanya tare da yin artabu da ‘yan sanda.

Mutane biyar ne suka mutu, ciki har da wani jami'in 'yan sanda na Majalisar wanda ake binciken mutuwarsa a matsayin kisan kai da kuma wani dan sanda ya harbe daya daga cikin masu zanga-zangar har lahira.

Sanatoci 100 - 'yan Republican 50 da 'yan Democrats 50 - da ke sauraren karar tsige shugaban mai wa'adi daya, suna cikin wani matsayi na musamman: da yawa daga cikinsu sun kasance shaidu ne kan hargitsin da ya faru a ranar 6 ga watan Janairu, yayin da suka tsere daga zauren majalisar dattijai domin kare kansu.