Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Amurka Bata Dage Takunkumai Kan Iran Ba Zamu Mutunta Yarjejeniya Ba-Ayatollah


Iran's Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei delivers a televised speech, in Tehran, Iran, Jan. 8, 2021.
Iran's Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei delivers a televised speech, in Tehran, Iran, Jan. 8, 2021.

A yau Lahadi shugaban addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga Amurka da ta dage duk wasu takunkumai a ka Iran indai har Washington na son Tehran ta ruguza shirinta na kera makaman nukiliya.

“Iran ta cike hsarudanta karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 amma Amurka da kawayenta basu cika nasu ba, dan haka idan suna so Iran ta sake biyewa yarjejeniyar, Amurka ta fara dage takunkuman,” a cewar wani sako da Khamenei ya kafa a shafinsa na twitter.

Ya rubuta cewa idan muka tabbatar da an dage dukkan takunkuman, to mu kuma zamu sake yin biyayya ga yarjejeniyar.

Shugaban Amurka Joe Biden da ya karbi ragamar shugabanci a watan da ya gabata, ya ce idan Iran ta koma ga yin biyayya ga yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, itama Amurka zata biyo sawu kana ta tsaya kan haka ta fadada yarjejeniyar da ka iya takaitawa Iran shirin kera makamai da ayyukanta a yankin.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar tsakanin Iran da manyan kasashen duniya guda shida a shekarar 2018 kana ya kakaba takunkumai a kan Tehran.

Iran, a hankali ta karya ka’idodin yarjejeniyar a wani matakin martani ga tsananin matsin lambar manufofin Trump, amma ta yita fadin cewa zata sake ci gaba da mutunta sharudan cikin hanzari idan Amurka ta janye takunkuman.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG