Hukumar yaki da almundahana ta gurfanar da ministan kan zargin bayanai ba dai-dai ba kan gidaje, da duk kuwa sabuwar tuhumar da ta kai caji shida ta kai darajar kudi Naira Miliyan 864.
Tuni lauyan Sanata Bala, Chiris Uche, ya bukaci bada belin tsohon ministan, sakamakon beli da aka bashi kan tsohuwar tuhuma, Uche ya nuna gamsuwa ga abin da yace kotun ba ta kawo wasu lamura masu sarkakiya ba.
Lauyan EFCC, Ben Ikani, yaki amincewa da bada belin Bala, yana mai cewa hakan zai shafi aikin hukumar da doka ta daura mata. Yace akwi zargin bada shaida ta barauniyar hanya kan wani gida da darajarsa ma ta kai fiye da rabin Naira Biliyan ‘daya.
Mai shari’a zai duba yiwuwar bada beli kafin ci gaba da gudanar da shari’ar. Hukumar EFCC dai ta rike tsohon Sanatan a lokuta mabanbanta, inda magoya bayansa kan yi tururuwa zuwa hedikwatar hukumar dan jajantawa.
Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5