Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wai Wasu 'Yan Matan Chibok dake Hannun 'Yan Boko Haram Ba Sa Son Dawowa


Shugaba Muhammadu Buhari Da 'Yan Mata 82 Da ;Yan Boko Haram Suka Sako
Shugaba Muhammadu Buhari Da 'Yan Mata 82 Da ;Yan Boko Haram Suka Sako

Rahotanni na nuni da cewa wasu cikin 'yan matan Chibok kusan 113 da suke hannnun 'yan ta'addan Boko Haram ba sa son dawowa wurin iyayensu lamarin da ba zai rasa nasaba da sabawa da kuma cusa masu akidar Boko Haram din ba.

Iyayen yaran nada ra'ayin koda da karfin tuwao a dawo masu da 'ya'yansu kamar yadda shugaban al'ummar Chibok dake Abuja ya bayyana.

Yace idan sun yadda da abun da wasu cikinsu suka ce to sun zama tamkar mahauta ke nan. Yana cewa su suna da hankali. Su 'yan Boko Haram din ai ba'a yadda dasu ba. Ko ta karfin yaya gwamnati ta kwatosu.

Inji shi bayan an dawo dasu an yi masu magani indan sun dage zasu koma hannun 'yan Boko Haram to a lokacin ba za'a ce an sacesu ba ne.

Akan cewa a dokar Najeriya idan mutum ya kai shekaru 18 yana iya zabar abun da yake son yi sai yace ko shekarunsu nawa dokar Najeriya bata bari mutum ya zauna da 'yan ta'adda ba.

Mai sharhi akan lamuran yau da kullum dake bin sawun 'yan matan tun lokacin da aka sacesu a shekarar 2014 Nasiru Gambo Malunfashi ya duba batun sabon 'yan matan da 'yan ta'adda. Yace yawancin yaran sun fito ne daga gidajen da basu da galihu. 'Yan ta'addan suna nunawa 'yan matan gata ne. Yace a duba 'yan matan 82 da aka sakosu. Da ganinsu an san ba cikin wahala suke ba.

Malam Nasiru yace kada a manta yaran sun yi fiye da shekara uku a hannun 'yan Boko Haram saboda haka dole sai an yi aiki a dawo masu da hankulansu kafin suyi rayuwa kamar ta kowa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG