Makasudin ware wannan Rana dai shine domin a tunatarwa al'umma mahimmancin Zaman Lafiya tare da kuma kawo karshen fadace fadace a tsakanin Jama'a daban daban. A sakon MDD na bana domin bukin wannan rana babban darakta a hukumar UNESCO, Irina Bokova, ta bayyana fatan da ake da shi na samun wanzar da zaman lafiya a duniya baki daya.
Wanda hakan shine zai kawar da cin zali da fadace fadace da yake yake a tsakanin al’umma, yayin da ya zamanto karfen kafa tare da haifar da ‘yan gudun hijira kimanin Miliyan 65. Taken bukin na bana shine ‘Wanzar da zaman lafiya tare da aiki da zaman lafiya kafada kafada da shirye shiryen MDD na ciyar da al’umma gaba.
Kama dai daga kan Najeriya zuwa wasu kasashen na gabas ta tsakiya har ma da tarayyar Turai da kasashen Amurka, rikici walau na ta’addanci ko kuma yanki na ci gaba da kawo cikas a kokarin da hukumomi da gwamnatoci ke yi na wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya daban daban.
A Najeriya dai rikicin Boko Haram shine ya zama karfen kafa wajen zaman lafiya da kuma ci gaban al’umma, inda yanzu haka MIliyoyin al’umma aka raba su da gidajensu tare da wanzar da Dubban ‘yan Gudun Hijira a sansanoni daban daban, da ma yanzu haka ke zaman jiran taimako daga gwamnatoci da al’umomi da ma kasashen duniya baki daya.
Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5