Shugabannin sun bude taron ne da batun ‘yan gudun hijira wanda suka ce ya zamewa duniya ‘daya daga cikin abubuwan da ke damunta. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi har da sakataren MDD Ban Ki-moon.
A jawabin shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, ya mayar da hankali kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa a kasar Sudan ta Kudu, yace irin wannan ne ya haddasa samar da ‘yan gudun hijira a sassa daban daban na duniya. Shugaba Buhari, ya bukaci shugannin biyu masu rikici tsakaninsu da su rungumi shirin sulhu, da aka cimma domin shine hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban ya bayyana takaicinsa yadda rashin zaman lafiya ya zamewa kasar alakakai, wadda duniya ta sa ran cewa kasar da jama’arta zasu sami ci gaba, yace domin inganta zaman lafiya ga sabuwar kasar a cikin taron MDD, akwai bukatar karin hadin kai tsakanin kasashen duniya, musamman ma kungiyar Tarayyar Afirka da sauran hukumomin kasashen duniya, wanda hakan zai bayar da damar aikawa da sojojin kiyaye zaman lafiya.
Domin karin bayani ga rahotan Ladan Ibrahim Ayawa.