Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zaman gaggawa yau Talata don tattauna halin da ake ciki a Gaza bayan mummunan fadan da aka yi tsakanin Isra’ila da Palasdinawa a cikin shekaru 5.
Daman dai da yawa daga cikin kasashe manyan kawayen Amurka irinsu Ingila, Faransa, Rasha da wasu kasashen Larabawa duk sun nuna rashin jin dadinsu da kudurin Amurka na bude ofishin jakadancinta a can birnin na Kudus, inda suka ce matakin na iya dada haddasa tashin hankali.
Gabanin taron Kuwait ta rubuta wata sanarwa tana nuna bacin ranta da takaicinta akan kisan Palasdinawa da yawa da dakarun Isra’ila suka yi, kasar ta kuma yi kira akan a gudanar sahihin bincike. Jami’an diplomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya sun ce Amurka, dake kasa kawar Isra’ila, da kuma kasashe biyar a kwamitin dake da ikon hawa kujerar na ki, sun dakile sanarwar.