Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Da Dama Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Dakile Borensu Da Israila Ta Yi


Falasdinawa dake zanga zangar kin amincewa da bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus
Falasdinawa dake zanga zangar kin amincewa da bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus

Harbin da jami'an tsaron Israila suka dinga yi akan Falasdinawa dake zanga zangar kin amincewa da bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus ya hallaka Falasdinawan da dama tare da jikata wasu sama da dubu biyu

Falasdinawa da dama ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da dubu biyu suka samu raunuka a arangamar da suka yi da dakarun Isra’ila akan iyakar Zirin Gaza, yayin da dubban masu zanga zanga suka yi ta bore kan bude sabon ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus.

Yayin da jami’an Amurka da na Isra’ila suke ta shagulgulan bude sabon ofishin diplomasiyan na Amurka, a wani yanki da bai kai nisan kilomita 100 daga wajen shagulgulan ba, an yi ta fama da gumurzu.

Dakarun Isra’aila sun ce akalla masu zanga zanga dubu 40 ne suka fito, yayin da jami’an kiwon Lafiya na Falasadinu suka ce an kashe masu zanga zanga 52 sanadiyar harbin bindiga da Amfani da hayaki mai sa kwalla.

Wannan rikici shi ne mafi muni da ya auku a yankin na Gaza, tun bayan yakin da aka yi da Isra’ila a shekarar 2014.

Yayin bude ofishin jakadancin na Amurka, an nuna shugaba Donald Trump a wani sako na hoton bidiyo, inda ya kira birnin na Kudus a “a matsayin babban birnin Isra’ila.”

Shi kuwa Firayi Ministan Isra’ilan, Benjamin Netanyahu ya ayyana cewa “Mun zo birnin na Kudus, kuma mun zo kenan.”

A wani bangaren kuma, da yawa daga cikin kawayen Amurka tare da abokanan hamayyarta, sun soki matakin bude ofishin jakadancin nata a birnin Kudus, suna masu cewa matakin zai kara rura wutar rikicin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fama da shi.

Kakakin Firayi Ministar Birtaniya, Theresa May, ya ce “ba mu amince da matakin da Amurkan ta dauka na kai ofishin jakadancinta zuwa birnin na Kudus ba tare da ayyana birnin a matsayin babban birnin Isra’ila, gabanin a cimma matsaya ta zaman Lafiya ta karshe a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, shi ma ya yi Allah wadai da rikicin da ya barke a yankin Gaza, inda dakarun Isra’ila suka kashe fararen hula falasdinawa sama da 50, yana mai cewa dama ya sha gargadi kan abin da ka iya biyo bayan matakin da Amurkan ta dauka na ayyana birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov ya kara nanata kin amincewarsu da matakin na Amurka, yayin da da yawa daga cikin shugabannin kasashen Larabawa su ma suka soki matakin, inda har firai ministan Lebanon, Saad Hariri ya kwatanta lamarin a matsayin “takalar fada” shi kuma ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Javad Zarif ya ce “wannan rana ce ta abin kunya.”

Ita ma Saudiyya ta yi Allah wadai da harin bindiga da aka rika kai wa akan Falasdinawa a yankin na Gaza, amma ba tare da ta ce uffan ba kan bude ofishin jakadancin na Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG