Yau Litinin ne za'a fara jigilar 'yan gudun hijira kashi na farko daga Maiduguri komawa zuwa garin Bama .
Kashin farko zai kunshi mutane dubu daya da dari daya ne. Garin dai 'yan Boko Haram suka daidaitashi tun shekarar 2014.
Garin Bama mai tazaar kilomita 70 da 'yan kai ya fuskanci rigingimun 'yan kungiyar Boko Haram da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba dubun dubata da muhallansu sakamakon cinnawa gidajen mutanen wuta lokacin da sojojin Najeriya ke kokarin fatattakar 'yan ta'addan daga garin.
Tuni dai gwamnatin jihar Borno ta ce ta kammala kimtsawa domin soma jigilar 'yan gudun hijiran rukuni na farko zauwa Baman, a wani kokarin rufe sansanin 'yan gudun hijiran dake Maiduguri da ma fadin jihar baki daya.
Alhaji Usman Jidda Shuwa shi ne sakataren gwamnatin jihar Borno, ya yiwa manema labarai bayani game da shirye shiryen fara jigilar 'yan gudun hijiran zuwa Bama. A cewarsa da zarar sun kammala maida mutanen Bama zasu fara maida mutanen Gwozah su ma.
Audu Jatau Muhammad, shugaban sake tsugunar da 'yan gudun hijiran ya ce yunkurin nasu kokarin gwamnatin jihar ne saboda basu samu taimako daga gwamnatin tarayya ba kamar yadda suka yi zato. Ya na ganin akwai dalilan siyasa a lamarin. Ya kira gwamnatin tarayya ta taimaka da kwalta a hanyar Bama daga Maiduguri.
Usman Zanna, kwamishanan ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ya ce sun dauki matakan da suka dace domin a maida mutanen gidajensu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5