Jiya wata kungiyar manoma shinkafa dake jihar Borno mai suna Walwani tare da taimakon babban bankin Najeriya ta kaddamar da dalar shinkafa a Maiduguri wanda shi ne irinsa na farko.
An kaddamar da dalar ne daga kananan hukumomi 12 dake kudancin Borno da wasu kananan hukumomi dake Borno ta tsakiya. Kungiyar na da manoma kusan dubu 18. An kaddamar da dalar ne a filin sukuwar dake Maiduguri.
Yayin kaddamar da dalar an yi kira ga matasa da su shiga harkar noma musamman noman shinkafa.
Gwamnan jihar Kashim Shettima ya ce noman shinkafar a jiharsa manuniya ce an soma samun zaman lafiya. Injishi abun da ake gani ya isa su godewa shugaban kasa da sojojin Najeriya. Ya na cewa idan babu zaman lafiya babu noma.
Alhaji Ali jagoran tafiyar a karkashin manoma shinkafa na gwamnatin tarayya ya yi karin bayani akan bazakolin da suka yi. Ya ce duk da matsalar tsuntsaye da rashin ruwa da hare haren 'yan ta'adda sun samu abun da zasu sayar su biya bashin banki da suka karba.
Alhaji Munir Ahmed babban jami'i ne a bankin noma na Najeriya kuma ya halarci taron ya yaba da abun da ya gani kuma wata dama ce ta samu wa matasan dake sha'awar shiga noman shinkafa.
Garahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum