Yau Kasashen Duniya Ke Tunawa Da Ranar Yaki Da Talauci

Yau 17 ga watan Oktoba ake bikin ranar yaki da talauci ta duniya, wacce ke matsayin wata damar tayarda gwamnatoci, da kungiyoyi daga barci akan maganar samar da hanyoyin fitar da jama’a daga kangin fatarar, sakamakon rashin wata kwakkwarar madogara.

Mutane miliyan 700 ne aka kiyasta cewa suna fama da talauci a yau, a duniya wadanda da kyar kowannensu ke samun dola 2 a kowacce rana. Bincike na nuni da cewa, 70 daga cikin 100 na wadannan matalauta na zaune ne a nahiyoyin Afirka, da Asia.

Ganin yadda talaucin iyaye ke shafar rayuwar ‘yayansu ya sa wannan karon Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen Duniya su maida hankali wajen tallafawa masu fama da talauci don ganin makomar irin wadanan yara ta kasance kyakkyawa.

Inganta rayuwar mata ta hanyar ba su jari domin gudanar da kananan sana’oi wani babban makami ne da zai taimaka a irin wannan yaki inji shugabar kungiyar ci gaban matasa ta JENOM Falmata Taya.

Mayar da hankali wajen noma, da kiwo ita ma wata hanya ce daban wajen taimakawar al’amuran yau da kullum, inji Massaoudou Ibrahim. Ya kara da cewa za ta taimaka wajen fitarda kasashen Afirka daga halin fatara da talauci.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da rabin matalautan da ake da su a yau a duniya na zaune ne a kasashen China, da Indiya, da Indonasia, da kuma Najeriya.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Yau Kasashen Duniya Ke Shagulgulan Ranar Yaki Da Talauci