Bikin wannan rana shine na 41 da za’a yi a Amurka bayan afkuwar bala’in rubzawar rijiyoyin mai a tekun yammacin Amurka da suka gurbata ruwan teku da harkokin noma da kamun kifi har da shi kansa yanayin illahirin yankin ruwan tekun. Yanzu ana gudanar da bikin tunawa da ranar alkinta yanayi a kasashe sama da metaan a duniya. A nan Amurka jami’an dake shirya bikin sun yi kira ga al’ummar kasa da kasa da su taimaka su bada cikakken hadin kan shuka itatuwa da furanni domin samar da iska mai lafiya ga mutane da dabbobi da cikakkiyar lafiyar yanayin zama.
A jawabin da yayi domin fara bikin na alkinta yanayi a Amurka, shugaba Barack Obama ya yaba da karfin halin dukkaan wadanda suka sanaya hannu domin karfafa mutumcin wannan rana tare da jaddada karfin alkawarin da Amurka tayi na shiga sahun gaban kasashen dake alkinta yanayi a duniya kuma yayi fatan Amurka zata ci gaba da rike matsayin ta wajen tinkrar kalubalen da sauye-sauyen yanayi ke haifarwa. Ita ma uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama ta shirya bada tata gudmmawar domin bunkasa muhimmancin wannan rana ta alkinta yanayi ta duniya wajen fita zuwa unguwannin talakawa domin tayasu tsaftace muhallinsu da kwashe datti daga kan tituna, koda yake an tsaida ayyukan saboda ruwan saman da ake yi a babban birnin na Amurka Washington D.C.