Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Amurka Ta Cimma Matsaya Data Hana Tsaikon harkokin Gwamnati


Shugaban Amurka Barack Obama yake magana bayan an cimma yarjejeniyar da ta hana tsaikon harkokin gwamnati.
Shugaban Amurka Barack Obama yake magana bayan an cimma yarjejeniyar da ta hana tsaikon harkokin gwamnati.

Ana saura ‘yan mintoci wa’adin ya kare,wakilan majalisar dokokin Amurka suka cimma ‘yarjejeniyar rage dubban miliyoyin dala daga kasafin kudi,in ba domin haka bad a harkokin gwamnatin tarayyar Amurka sun tsaya cik da karfe 12 dare.

Ana saura ‘yan mintoci wa’adin ya kare,wakilan majalisar dokokin Amurka suka cimma ‘yarjejeniyar rage dubban miliyoyin dala daga kasafin kudi,in ba domin haka bad a harkokin gwamnatin tarayyar Amurka sun tsaya cik da karfe 12 dare,watau karfe biyar na asubahin Najeriya Nijar da kamaru, da ma Cadi.

Shugaban Amurka Barack Obama yace yarjejeniyar da aka cimma a daren jiya jumma ta kunshi rage kudi mai tsanani na dala milyan dubu 38 daga kasafin 2011.

Majalisar dattijai d a ta wakilai sun amince da kuduri na mako daya da zai bada izinin ci gaba da aikin gwamnati,ana sa ran majalisar dokokin zata kada kuri’a kan kasafin kudin na bana a wajajen tsakiyar makon gobe.

Kakakin majalisar dokokin Amurka dan Republican John Boehner, yace an ja daga na tsawon lokaci,duk da haka yace yana da muhimmanci an rage kashe kudi domin samar da yanayi mai kyau don a kirkiro ayyukan yi.

Shi kuma da yake magana shugaban masu rinjaye amajalisar dattijai Harry Reid,yace an sha wuya kamin cimma daidaito,amma hakan yana da muhimmanci ga kasar. Yace yadda ya zamanto tilas ga Amurkawa su yi tsimi haka ma ya wajaba ga wakilai.

Idan ba domin an cimma dai-daito ba,da ma’aikatan gwamnatin tarayya kamar dubu dari takwas ne zasu yi zaman kashe wando,yayinda za’a dakatar da biyan sojojin Amurka.

XS
SM
MD
LG