Yau Cape Verde Za Ta San Makomarta Yayin Da Za Ta Hadu da Kamaru

'Yan wasan Kamaru suna atisaye

Tuni Kamaru ta tsallaka zuwa zagayen 'yan 16 da za a fara sallamar duk kasar da aka ci.

Kasar Cape Verde na shirin karawa da Kamaru a rukuninsu na A gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Bangarorin biyu za su hadu ne a filin wasa na Olembe da ke birnin Yaounde kasar a yau Litinin.

Tuni Kamaru ta shiga zagayen ‘yan 16.

Cape Verde kuwa na fatan ganin ta kai zagayen na ‘knockout’ tana kuma bukatar nasara ne idan har tana so ta cimma wannan buri.

'Yan wasan Cape Verde

A wasanta na baya, Caoe Verded ta sha kaye a hannun Burkina Faso da ci 1-0 bayan da ta yi nasara akan Ethiopia a wasan farko.

Ko da yake, ko da maki daya ta samu, za ta iya tsallaka wa zagayen na gaba, amma sai ta jira ta ga yadda wasan Burkina Faso da Ethiopia zai kaya.

Yanzu haka Kamaru ce a gaba a wannan rukuni da maki 6 sai Burkina Fa sao da ita Cape Verde da maki uku-uku.