Shugaba Amurka Donald Trump yayi jimamin wannan rana da safiyar yau a Fadar White House, kafin halartar taron tunawa da ranar a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ga iyalan wadanda aka kashe lokacin da 'yan ta'addar Al-Qaida sukayi fashin jirgin saman da aka yi amfani dashi wajen kaiwa ginin hari.
A birnin New York kuma, daruruwan wadanda suka tsira da dangin wadanda aka kashe sun taru ne a filin da harin ya faru da ake kira Ground Zero, inda tagwayen gine-ginen Cibiyar Cinikayya ta Duniya ya ke kafin jiragen fasinja biyu da al-Qaida ta kwace ikonsu ta kuma tarwatsa ginin.
Ana sa ran mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, zai halarci wasu bukukuwan a garin Shanksville, dake jihar Pennsylvania, kusa da inda jirgin United Flight 93 ya fadi bayan fasinjoji suka karbe iko daga hannun ‘yan ta’addan da suka sace jirgin.
Maza goma sha tara ne 'yan kungiyar al-Qaida su ka yi fashin jiragen guda hudu.
Harin wanda shine mafi muni da aka kaiwa kasar Amurka tun daga yakin Pearl Harbor a shekara 1941, hare-haren da suka faru a 11 ga watan Satumba, sun canza ra'ayin Amurka game da harkar tsaro kuma ya sanya tsohon Shugaban Amurka George W. Bush kaddamar da yaki da ta'addanci da kuma mamaye kasar Afghanistan.