Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce korar da shugaban kasa Donald Trump ya yi wa mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa John Bolton, ba za ta sauya manufofin Amurka a kasashen waje ba.
“Ba na tunanin wani Shugaba a duniya zai yi tsammanin cewa saboda wasunmu sun tafi, manufofin shugaba Trump za su sauya ta kowace irin hanya,” inji Pompeo.
Shi dai Pompeo ya bayyana a gaban manema labarai tare Sakataren Baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin, domin ganawa kan ‘yancin an gashin-kai da shugaban Amurka ke da shi na daukan matakan saka takunkumi a yakin da yake yi da‘ayyukan ta’addanci.
A baya an tsara tare da Bolton za su yi ganawar, kamar yadda aka sanar a baya, lamarin da ya yi nuni da hanzarin ficewar Bolton daga gwamnatin ta Trump.
Da tsakar ranar Jiya Talata Shugaba Trump ya wallafa bayanan sallamar Bolton a shafinsa na Twitter, inda ya ce, “na fadawa Bolton a daren jiya cewa, ba na bukatarsa a White House, domin ba na gamsuwa da irin shawarwarin da yake bayarwa, saboda haka, na ce ya mika takardar yin murabus, wacce ya ba ni da safiyar (jiya) Talata.”
Sai dai a martanin da ya mayar cikin gaggawa, a shafin na Twitter, Bolton ya ce, “ni ne na mika bukatar zan ajiye aikina, sai Shugaba Trump ya ce min za mu tattauna da safe.”
A halin da ake ciki, an nada Charlie Kupperman, a matsayin mukaddashin mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa, a cewar fadar ta White House.
Facebook Forum