A cewar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya, Wafula Chebukati, “Bisa ga tabbacin bayanan da wasu hukumomi da jami’an tsaro suka gabatarwa da hukumar, za a gudanar da zabe yau Alhamis 26 ta watan Oktoba kamar yadda aka tsara.”
Amma shugaban jam’iyyar adawar Kenya, Raila Odinga, wanda ya janye kansa daga zaben a farkon watannan, ya yi kira ga magoya bayansa a jiya Laraba da su kauracewa zaben.
Da safiyar jiya Laraba ne babban alkali kasar David Maraga, ya fada cewa alkalai biyu ne kadai suka je kotun cikin alkalai bakwai da ake da su, hakan ya gaza adadin alkalai biyar da ake bukata don yanke hukunci.
Haka kuma wani alkali yace nade-naden jami’an hukumar zaben da aka yi don zaben na yau, ba a yi su bisa ka’ida ba.
Sai dai kuma hukumar zaben ta Kenya ta ce nade-naden na bisa ka’ida, kuma jami’an zasu gudanar da harkokin zaben shugaban kasar na yau.