Yau Ake Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi 44 a Jihar Kano, Amma Jami'an Tsaro Sun Kama Mota da Jebun Kuri'u

Mata suka shiga layi a zaben shugaban kasa da ya shige a Najeriya.

Shugaban hukumar zabe ta jihar kano Dr. Sani Lawal ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai.
Yayin da za'a fara kada kuri'a domin zabar shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano wani lokaci a safiyar yau Asabar, hukumar zabe mai zaaman kanta ta jihar tace jami'an tsaro sun kama wata motar dakon kaya makare da kuri'u na jabu a yankin kudancin jihar.

Shugaban hukumar Dr. Sani Lawal Malumfashi ya sanar da haka ga taron manema labarai a Kano.

Wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya bamu rahotan cewa, kimanin makonni uku da suka gabata jami'ai sun kama wani mutum yana sojan gona yana karbar kudade daga hannun matasa bisa alkawarin cewa, zai basu aikin zabe a hukumar.

Mataimakin sifeton 'yan sandan najeriya mai kula da shiyya ta daya dake Kano Alhaji Tambari Yabo Mohammed yace jami'an tsaro sun shirya sosai domin tabbatar da doka da oda a yayi da kuma bayan kammala zaben.
zaben na yau shine zai kawo karshen mulkin kantomomi a kananan hukumomin na jihar Kano 44 tun shekara ta 2010.